Shugaba Barack Obama na Amurka ya tuna ranar cikar shekara guda da mutuwar shugaban kungiyar al-Qa’ida, Osama bin Laden, ta hanyar kai gajeruwar ziyara zuwa Afghanistan, da sanya hannu kan yarjejeniyar dangantaka da kasar tare da mika sako ga Amurkawa a wannan shekara ta yin zaben shugaban kasa cewa yakin Afghanistan yana dab da karewa.
A cikin jawabinsa da aka nuna ta telebijin daga wani sansanin mayakan sama dake can nisan duniya da Amurka, Mr. Obama yace Amurka ta shafe shekaru fiye da 10 cikin bakin hayaki na yaki. Amma ya kara da cewa a yanzu ta fara hango hasken rana.
Shugaban ya fadawa Amurkawa cewa a yanzu ana iya cimma gurin kawar da kungiyar al-Qa’ida. Yace wannan yaki ya faro daga Afghanistan ne, kuma a nan zai kare.
Shugaban yayi magana ne a bayan da ya sanya hannu a kan Yarjejeniyar Kawance da takwaran aikinsa na Afghanistan, Hamidu Karzai.
Yarjejeniyar ta shafi batutuwan tsaro, tattalin arziki da mulki tare da zayyana irin dangantakar da zata kasance a tsakanin Amurka da Afghanistan a bayan an janye akasarin sojojin NATO daga kasar a 2014.
Yarjejeniyar zata kyale Amurka ta bar wasu ‘yan sojoji kadan a Afghanistan domin horas da sojojin kasar tare da ci gaba da farautar ‘yan al-Qa’ida. Kungiyar ta’addancin ta fi karfi yanzu a kasar Pakistan, inda ‘ya’yanta kalilan ne kawai a cikin Afghanistan.