Shugaba Ali Bongo na kasar Gabon yace zai mika dukkan kudin da ya gada daga mahaifinsa, tsohon shugaba Omar Bongo, ga wata gidauniyar matasa da za a kafa musamman domin matasan kasar, yayin da zai kuma mika wani ginin dake Libreville babban birnin kasar domin gina jami’a.
A bayan wadannan kuma har ila yau, akwai wasu kadarori guda biyu na marigayi Omar Bongo dake Paris, babban birnin Faransa wadanda su ma za a bayar da su ga kasar.
A lokacin da yake jawabi na bukin cikar shekaru 55 da samun ‘yancin kan kasar Gabon, shugaba Bongo yace a idanunsa, duk ‘yan kasar magadan marigayi shugaba Omar Bongo ne.
Wannan mataki na shugaba Ali Bongo, yana zuwa a daidai lokacin da alkalai a kasar Faransa suke ci gaba da binciken iyalan marigayi Omar Bongo bisa zargin yin rub da ciki a kan dukiyar kasarsu, zargin da suka ce atafau bah aka ba ne.
An yi shekara da shekaru ana zargin marigayi Omar Bongo da laifin handama, inda a shekarar 2010, Faransa ta kaddamar da wani bincike kan satar dukiyar gwamnati bisa matsin lamba daga kungiyoyi irinsu Transparency International.
Har yanzu dai ba a aiwatar da wasiyyar marigayin ba, wanda yam utu a shekarar 2009, bayan yayi mulkin shekaru 41 a kasar Gabon. An ce ya bar dukiya ta miliyoyin dalolin Amurka.