Shirin Taron Tattalin Arziki Yayi Nisa

  • Ibrahim Garba

Ngozi Okonjo-Iweala ministar Ma'aikatar Kudin Najeriya

Gwamnatin tarayya da wasu sun yi nisa da shirin taron tattalin arziki na kasa da kasa da za'a fara a Abuja ranar Laraba
Gwamnatin Najeriya da hukumomi masu kula da tattalin arzikin duniya baki daya sun yi nisa da shirin kasaitaccen taron tattalin arzikin duniya da za'a fara yi a Abuja ranar Laraba.

Taron zai duba yadda za'a bunkasa sha'anin albarkatun kasa da samarda ayyukan yi da kuma tattalin arzikin kasashen Afirka da dama ganin irin matsaloli na talauci da rashin aikin yi da suka yiwa yankin katutu.

Taron mai taken "Haduwa Domin Fitar da Alkibla Daya ta Yakar Talauci Domin Tabbatar da Cewa An Samu Ayyukan Yi" yana zuwa ne daidai lokacin da ake ganin samarda aikin yi da talauci sun addabi kasashen Afirka da dama.

Daidai lokacin da ake tunanin alkiblar da taron zai karkata wani masanin tattalin arziki Malam Sha'aibu Idris yana ganin cewa kodayake taron yana da tarihi mai karfin gaske an fara shi ne daga kasashen da suka cigaba kuma suna kokarin kawar da kasashensu daga karayar tattalin arziki. An kawoshi Afirka ne yanzu domin kasashen nahiyar su nemi hanyoyin da zasu bunkasa tattalin arzikinsu ta hanyar nuna irin albarkatun da suke dashi domin kasashen waje su saka jari.

Amma duk wadannan suna tare da kalubale. Kusan shekaru 15 da suka gabata kasashen duniya suka fara hangen cewa nan gaba tattalin arzikin duniya zai koma kasashen Afirka domin nan ne ake da ma'adanai da kasashen noma da jama'a da yawa. Ga mai hankali wannan taron za'a yi ne a sha shayi da cin kaji a watse. Da wuya ya kaiga wani abu na alfanu.Yace duk mai hannu da shuni zai saka jari ne inda zai anfana. A kasar Najeriya har yanzu ana fama da halin kakanikayi domin babu tabbacin tsaro da kwanciyar hankali. Akwai matsalar sufuri da wuta. Ban da haka talauci ya yiwa kasar kanta. Babu shakka kasar tana da jama'a fiye da miliyan 160. Amma kusan miliyan 150 basu iya kashe dalar Amurka biyu a yini guda. Idan an sarafa kaya shin ina kudin da mutane zasu saya da su

Kawo yanzu mutane a Abuja sun shiga wani kuncin rayuwa sabili da matakan tsaro da aka dauka domin kada a kai hari birnin lokacin taron.

Ga rahoton Umar Faruk Musa

Your browser doesn’t support HTML5

Shirin Taron Tattalin Arziki Yayi Nisa - 4' 25"