Shirin Sauya Fasalin Naira: Masu Sayen Amfanin Gona Na Sayen Kayan Abinci Kudi Hannu

Kayan Amfanin Gona

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, masu sayan amfanin gona a kakar bana, na bin manona har gonakinsu suna cinikayyar kayan abinci da manoman suka samar, inda suke biyan duk abin da suka saya kudi a hannu

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kwararru ke hasashen cewa, akwai yiwuwar a ‘yan makonni masu zuwa, bankunan kasar su fuskanci cunkoson jama’a da ke muradin aje kudade, sakamakon tsarin babban bankin Najeriyar na sauya fasalin wasu daga cikin takardun kudaden kasar.

Kimanin makonni uku da suka shude ne babban Bankin Najeriya ya sanar da yunkurinsa na sauya fasalin uku daga cikin takardun kudin kasar, wato Naira 200 da naira 500 da kuma naira 1000.

Faduwar darajar Naira

A tsakiyar watan gobe na Disamba ne ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabbin takardun, inda za’a ci gaba da amfani da su kafa da kafa da tsoffin takardun zuwa karshen watan Janairun badi.

Sabanin yadda aka yi hasashe, ya zuwa yanzu bankunan kasuwanci a sassan Najeriya sun ci gaba da kasancewa yadda suka saba ba tare da cunkoson jama’a ba.

Ko da yake. Malam Aliyu Wada Nas, shugaban shugaban reshen jihar Kano na Cibiyar kwararrun ma’aikatan bankuna ta Najeriya ya tabbatar da wannan yanayi, amma ya ce akwai yiwuwar sai wa’adin da gwamnati ta bayar ya kusa karewa ne mutane za su fara jerin gwano a bankuna domin sanya kudadensu a asusun banki, domin kuwa hakan na daya daga cikin halayen ‘yan Najeriya.

Malam Aliyu Wada Nas

Baya ga bankuna, an yi tsammanin cewa, za’a rinka ganin jerin gwanon mutane a kananan cibiyoyin karba da biyan kudade na zamani da ake kira POS, sanadiyyar waccar sanarwa ta sauya takardun kudi na naira.

Amma Malam Abdulkarim Sani, na Cibiyar POS ta Bello Kano da ke Zoo Road a Kano, ya ce, sanarwar babban bankin kasa CBN ba ta kawo wani sauyi dangane da yadda hada-hadar ajiyar kudi ke gudana a Cibiyoyin POS ba.

Amma mai yiwuwa ne, hakan ba ya rasa nasaba da yadda wasu daga cikin masu kudin a hannu ne suka karkata akalar su wajen sayen amfanin gona a kauyuka.

Alhaji Ali Yunusa ‘Yandutse shugaban kungiyar manoma da masu sayar da amfanin gona ta Amana a jihar Jigawa ya ce, yanzu haka baki na kwarara gonakin manoma suna sayan amfanin da aka noma, al’amarin da ya sanya kayan abincin suka ninka farashin sun a baya.

Amma ya ce su a fahimtarsu, hakan na da alaka da kudirin shugaban kasa na sauya fasalin wasu daga cikin takardun kudi na naira.

Saurari cikakken rahoto cikin sauti da ga MAHMUD IBRAHIM KWARI

Your browser doesn’t support HTML5

NAIRA REDESIGN & MONEY DEPOSITORS.mp3