Biyo bayan takaddama kan shirin nan na tsugunar da makiyaya wuri guda da gwamnatin tarayya ta yi wa lakabin ‘’Ruga Settlement’’, a turance, al’ummomin da abin ya shafa kai tsaye sun ba da shawarwari kan matakan da gwamnati ya kamata ta bi kan shirin.
Architect Macham Makut, jagoran matasan yankin Bokkos, a jihar Filato, ya ce kamata ya yi gwamnati ta zauna da al’ummar wurin da ta kebe don shirin, saboda su sami fahimta da ba da shawarar bai wa makiyaya tallafin da za su kebe dabbobinsu a shinge.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah, reshen jihar Filato, Alhaji Nura Muhammad ya ce gwamnati ta yi koyi da abin da tsohon shugaban kasar Libya ya yi, na mai da hamada.
Kafin dakatar da shirin na Ruga ko akasin haka, gwamnan jahar Filato, Simon Lalong ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa, shirin zai kyautata wa duk ‘yan Najeriya ne.
Har yanzu dai gwamnati bata fito fili tayi bayanin yadda zata aiwatar da shirin ba.
A saurari cikakken rahotun wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5