Shirin Nada Sarki Charles III A Birtaniya

Sarki Charles III

Birtaniya na shirye-shiryen nadin sarautar Sarki Charles III, wanda zai gudana a ranar Asabar. An gayyato shugabannin duniya da dama da shugabannin kasashe zuwa wannan taron mai dimbin tarihi, yayin da ake sa ran miliyoyin mutane za su kalla ta talabijin.

Za a yi bikin ne a Westminster Abbey na Landan, inda aka yi jana'izar mahaifiyar Charles, Sarauniya Elizabeth ta biyu a watan Satumba bayan rasuwarta ta na da shekaru 96.

Justin Welby, Archbishop na Canterbury, zai jagoranci hidimar nadin sarautar na tsawon sa'o'i biyu. Kamar yadda aka saba bisa al’ada zai nemi wadanda ke halartar hidimar da miliyoyin masu kallo a talabijin su yi mubaya'a da karfi ga Sarki Charles, tare da fadin wadannan kalmomi: "Na rantse cewa zan yi mubaya'a ga Mai Martaba, kuma zuwa ga wadanda aka gada bisa ga doka. Don haka Allah ya taimakeni."

A karon farko, hidimar za ta hada da bishop mata da shugabannin wasu addinai.

Dubban daruruwan mutane ne ake sa ran za su yi layi daga fadar Buckingham zuwa Westminster Abbey. Charles, da matarsa, Sarauniya Consort Camilla, za su yi tafiya a cikin wani kayataccen abin hawa mai ado lu’u lu’u zuwa hidimar.

Charles zai zauna a kan kujerar sarauta, wadda aka yi amfani da ita wajen nadin sarautar Biritaniya sama da shekaru 700. Yana rufe Dutsen Scone, wani tsohon dutsen biki da Sarki Edward I ya kama daga Scots a shekara ta 1296.

Za a shafa wa sarkin da wani Mai da aka kawo daga birnin Kudus. Gicciyen da za a yi amfani da shi yana kunshe da baraguzan da aka ce an tattarosu ne daga gicciyen Yesu na ainahi, wanda Paparoma Francis ya bayar.