Shirin N-Power Zai Fara Karbar Takardun Neman Aikin Malanta Dubu 500

A matakin farko na aiwatar da sabon shirinta na tallafawa matasa da zai lashe kudi har naira miliyan dubu 500, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari zata fara karbar takardun neman gurabu guda dubu 500 na malanta daga matasan da suka kammala karatun jami’a, kuma za a mika takardun neman aikin ne ta kan intanet a wani shafi na musamman da aka kirkiro don wannan mai adireshin: npower.gov.ng

Za a kaddamar da wannan shafi na karbar takardun neman aikin a ranar asabar 11 ga watan nan na Yuni, amma sai a ranar 12 ga wata ake sa ran takardun neman aikin zasu fara shiga.

Gwamnati ta yi kira ga matasa ‘yan Najeriya wadanda bas u da aikin yi da su ziyarci wannan shafi domin mika takardunsu na neman aikin koyarwa.

Wannan shirin daukar matasa dubu 500 a zaman malamai, wanda aka sanya ma lakabin N-Power Teach, shine na farko daga cikinw asu shirye shiryen samar da ayyukan yi da horaswa guda uku wadanda ‘yan Najeriya zasu fara cin moriyarsu daga ranar lahadi 12 ga watan nan.

Sauran biyun sune N-Power Knowledge wanda zai horas da ‘yan Najeriya su dubu 25 kan fasahar zamani. Sai kuma shirin N-Power Build wanda zai horas da wasu ‘yan Najeriyar su dubu 75 a fannoni irinsu gine-gine, makanikanci, kula da hotel hotel ko wuraren sayar da abinci, ayyukan sarrafa goran ruwa da gas. Dukkan wadanda zasu samu horaswar, zasu rika samun albashi a lokacin da suke cikin wannan shiri na horo.

Matasa dubu 500 da za a dauka aikin koyarwa, zasu rika samun albashin dubu 23 a wata, sannan za a rarraba musu na’urorin kwamfuta dauke da duk bayanan da suke bukata domin gudanar da ayyukansu.