Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsaftar Halayen Matasa Jarin Su A Rayuwa!


A wani bincike da wasu masana suka gudanar, da ya bayyanar da wadansu halaye da yakamata ace kowane matashi yana dasu, musamman idan akazo maganar karatu ko neman aiki, da kuma samun dacewa da duk abun da akasa a gaba. Idan kuwa har mutun bai lakanci wadannan halayyan zaman takewa rayuwa ba, lallai mutun kan iya samun kan shi cikin wani hali na rayuwa.

Abu na farko shine a samu mutun nada halin sauraren mutane idan suna magana, kada mutun ya amsa, har sai bayan mai magana ya gama. Hakan zai ba mutun damar fahimta cikin natsuwa da bada gudunmawa mai inganci. Sai mutun ya dinga amfani da lokaci yadda ya kamata, tsara abubuwa da mutun zai yi da bada lokacin kawane abu shima abune mai matukar taimakawa wajen gogewa a zaman duniya.

Uwa uba shine, mutun ya zama ma’abuci gaskiya a kowane hali ya samu kanshi, idan akayi ma mutun magana, yayi tunani kamin ya bada amsar da ta dace da tambayar. Nazari kodai na littatafai ko na tarihin magabata, don duba yadda suka gudanar da rayuwar su a lokacin su, hakan na taimakawa matuka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG