A wannan makon, shirin kasuwa a kai maki dole ya kai ziyara kasuwar Mile 12 da ke tsakiyar birnin Legas don jin tarihin kasuwar da kuma kalubalen da 'yan kasuwar ke fuskanta
WASHINGTON, D.C —
Shehu Usman, shi ne shugaban kasuwar Mile 12, ya ce kusan shekara 40 kenan da kafa kasuwar wadda ta shahara wajen saida kayan gwari kuma kasuwa ce da kayayyaki ke shigowa daga sassan Najeriya dabam-daban har ma da wasu kasashen yammacin Afrika.
'Yan kasuwar sun ce babban kalubalen da suke fuskanta a harkokinsu shi ne rufe iyakokin Najeriya, wanda ya janyo hauhawar farashen kayayyaki.
Saurari cikaken shirin daga Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5