Shirin gurfanar da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, da dan uwansa, Ahmad Sirika, akan wata sabuwar tuhumar zambar Naira biliyan 19 da miliyan 400 bai yi nasara ba sakamakon rashin bayyanar wadanda ake kara a kotun a yau Talata, wadanda aka ce ba sa Abuja.
Lauyan Hukumar EFCC, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati, Oluwaleke Atolagbe, ya shaidawa alkalin kotun, Mai Shari’a Suleiman Belgore, cewar ba’a mikawa tsohon ministan da kaninsa sammacin dake kunshe da tuhumar a cikinsa ba.
Don haka, ya bukaci kotun ta dage zamanta, bukatar da alkalin ya amince da ita.
Daga bisani Mai Shari’a Belgore ya sanya ranar Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki, domin sauraron karar.
A wannan karon EFCC ta maka tsohon ministan da dan uwansa a kotu ne, akan wasu tuhume-tuhume 8 masu nasaba da zambar Naira biliyan 19 da miliyan 400.
Ana zargin kudaden na dimbin kwangilolin da tsohon ministan sufurin jiragen saman ya baiwa kamfanin “Enginos Nigeria Limited”, wanda mallakin kaninsa, Ahmad ne.
A Alhamis din data gabata, 9 ga watan Mayun da muke ciki, Hadi Sirika ya gurfana gaban Mai Shari’a Sylvanus Orji, tare da diyarsa Fatima da sirikinsa, akan zargin badakalar Naira biliyan 2 da miliyan 700.
Dukkaninsu sun ki amsa laifin da ake tuhumarsu akai kuma a halin yanzu an bada belinsu.