Shin Za'a Kwato 'Yan Matan Chibok Kuwa

Kungiyar "Bring Back Our Girls" dake fafitikar ganin an sako 'yan matan Chibok

Tun sha hudu ga watan Afirilun wannan shekarar aka sace 'yan matan Chibok daga cikin makarantarsu amma har yanzu shiru a ke ji kamar an shuka dusa

Wani Dapani Yanga yana da danginsa guda bakwai da aka sace cikin 'yan matan. Yace bakwai daga kauyensa suka fito. Uku cikinsu 'ya'yan 'yan uwansa ne.

Dapani yace har yanzu basu fitar na ran ganin an sako 'yan matan ba. Su ma 'yan kungiyar "Bring Back Our Girls" da suke zaman durshen a Abuja tare da fafitikar ganin an sako 'yan matan sun ce ba zasu daina ba har sai an sako yaran.

Aisha Yusuf daya daga cikin jigajigan kungiyar tace kamar ana son a manta da yaran gaba daya ne. Gwamnati na zargin kungiyar da tunashe da jama'a batun yaran sabili da dagewar da suka yi. Mako biyu bayan an sace yaran kungiyar ta fara zaman durshen. Kawo yanzu basu daina ba. Kullum suna zaman durshen. Babu ranar da suka fasa duk da barazanar da 'yansanda keyi masu. Aisha tace har yanzu akwai 'yan mata 219 da ba'a san inda suke ba. Kada duniya ta manta. Haka ma yaran makarantar Buni Yadi 59 da aka gille kawunansu. Yau babu wanda yake batunsu. Zasu cigaba da zaman har sai ranar da aka sako yaran.

Abubakar Yusuf dan kungiyar "Bring Back Our Girls" ya bayyana takaicinsa ne da yadda batun tsaro ya wuce karfin mahukuntar kasar. Maganar tsaro ba magana ba ce da wani zai ce a tausaya masa. Yakamata shugaban kasa yayi abun da ya dace.

Amma shugaban bayyana manufofin gwamnati Mike Omeri yana cewa ba gaskiya ba ne gwamnati ta manta da batun 'yan matan da aka sace ba. Zata cigaba da kokarin cetosu.

Amma da irin abun da ire-iren Mike Omeri ke fada, ana ganin gwamnati tana yiwa batun 'yan matan rikon sakainar kashi.

Ga rahoton Madina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Shin Za'a Kwato 'Yan Matan Chibok Kuwa - 3' 24"