Babbar jam’iyar adawa ta PDP a Najeriya na gudanar da babban taronta a Abuja, babban birnin kasar.
Taron zai mai da hankali ne wajen zaben shugabannin da za su ja ragamar tafiyar da al’amuran jam’iyar na wasu shekaru masu zuwa.
Mukamin kuma da ya fi jan hankali shi ne na shugaban jam'iyar.
Wannan babban taro shi ne na farko tun bayan da jam’iyar ta sha kaye a hannun jam’iyar mai mulki ta APC a shekarar 2015.
Tun gabanin taron alamu sun nuna gwamnonin jam’iyar, musamman gwamna jihar Rivers, Ezenwo Nyesom Wike na mara baya ga dan takarar shugabancin jam’iyar Uche Secondus.
Hakan ya sa wasu daga kudu maso yammacin kasar suke ganin hakan zai iya shafar sabon hadin kan jam’iyar.
Shi dai Secondus ya fito ne daga kudu maso kudancin Najeriya.
Masu lura da al'amura na ganin wannan taron zai zamanto tamkar zakaran gwajin dafi ne ga sabon hadin kan da jam'iyar ta samu.
Tuni dai Bode George, ya bayyana cewa ba za a yi “wannan kwamacalar da shi ba.”
Ya kuma janye takararsa, inda ya ce ya kamata gwamna Wike ya bai wa Yarbawa hakuri, yana mai cewa ya ci musu zarafi.
Bayani sun yi nuni da cewa sakamakon taron zai iya kai har zuwa dare kafin a same shi.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya domin samun cikakken bayani:
Your browser doesn’t support HTML5