Shin Ya Dace Mai Martaba Sarkin Kano Ya Cigaba da Irin Kalamunsa

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Mai Martaba Sarkin Kano ya kan bayyana duk abun da yayi imani dashi ba tare da wata rufa rufa ba musamman abubuwan da suka shafi harkokin kudi, tattalin arziki da cigaban al'umma.

Wannan halin nasa ya kan jawo tsokaci daga wadanda suke ganin bai dace ya dinga yin wasu kalamu ba da wadanda suke ganin kalamunsa sun dace idan an yi la'akari da irin ilimin da yake dashi.

Babban editan jaridar yanar gizo ta Daily Nigeria Jafar Jafar yayi rubutu mai tsawo yana jawo hankalin Sarkin.

Inji Jafar Jafar duka hannunka mai sanda ake yiwa shi Mai Martaba domin babu wanda yake son a ce ga sarkinshi ya shiga wani hali da bai dace a ce ya samu kansa a ciki ba. Yace yadda suka goyi bayan nadinsa haka ma ba zasu bari ya shiga wani hali da zai bata masa rai ko ya jawowa al'umma bacin rai ba.

Malam Jafar Jafar yana ganin Sarki Muhammad Sanusi II tamkan ma'aikacin gwamnati ne. Saboda haka akwai maganganun da bai kamata a ce yana yinsu ba, musamman akan gwamnati. Yace tarihi ya nuna cewa duk sarakunan da aka cire baya wuce takunsaka da suka samu da gwamnati.

Amma ga shugabannin al'umma irinsu Alhaji Abba Dan Masanin Fika yace abun da yake janyo cecekuce shi ne canzawar alamura. Yana mai cewa yadda aka dauki sarauta da, da yadda aka dauketa yanzu ba daya ba ne. Shekaru hamsin da suka wuce basarake bai cika magana ba, amma in yayi magana ita ce ta karshe, injishi. Yace yanzu Allah ya kawo wani zamani inda Sarki Sanusi yana da ilimin zamani yana kuma da na addini. Yace cikin sarakuna irinsu Sanusi basu da yawa.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shin Ya Dace Mai Martaba Sarkin Kano Ya Cigaba da Irin Kalamunsa - 2' 53"