Shin me ya haddasa faduwar kasuwar hannun jari a Najeriya

Ministar harkokin kudin Najeriya

Cikin watan Janairun nan da ya gabata kasuwar saka hannun jari a Najeriya ta yi hasarar Nera tiriliyon daya da miliyan dubu dari shida da talatin, wato jimillar abun da suka saka jari ke nan suka yi hasararsa

Ganin cewa hasarar da masu saka jari a kamfuna suka tafka a kasuwar hada-hadar hannun jarin Najeriya ya sa Muryar Amurka ta bi digdigin musabbabin aukuwar lamarin.

Hassan Maina Kaina ya samu ya zanta da Malam Jibirin Agade Agabi wanda ya bayar da dalilai uku da suka haddasa hasarar.

Malam Agabi yace akwai abubuwa da yawa da suka faru. Dalili na farko wanda kuma tamkar ya shafi duniya gaba daya shi ne faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya. Kowa ya sani cewa Najeriya ta dogara ne, kusan kacokan akan man fetur domin samun kudin shiga. Banda haka kusan duk abun da kasar ke anfani dashi hatta abinci sai an sayo daga waje. Yanzu da babu dala kamar yadda aka saba da can abubuwa sun yi wuya saoda rashin kudi.

Wata hanya kuma da dala ke shiga kasar itace ta hannun mutanen kasashen waje dake shigo da kudinsu su saka jari. Su ma sun ja baya saboda suna ganin tattalin arzikin kasar ya samu rauni saboda faduwar farashin man fetur. Wannan ya sa babu kudin dake shiga kasuwar kamar da domin sayen hannun jari.

Wani dalili kuma shi ne saukin samun kudin biyan bukata da hannun jari ke dashi ya sa kasuwar ta fadi. Misali da wuya lokacin karancin kudi mutane su sayar da gidaje a saukake ko ma wasu kadarori. To amma idan mutum nada hannun jarin kamfani yana iya sayar da kadan ciki ya biya bukata koda ma zai sayar kasa da yadda ya saya.

Dalili na uku shi ne yadda masu saka jari daga cikin gida da na waje duk sun mayar da hankalinsu ne akan kasuwar hannun jari. Su na waje kokari su keyi su sayar da hannayen jarin da suke rike dasu ko nawa ne su fice. Na cikin gida kuma suna neman hanya mafi sauki da zasu biya bukatunsu. Saboda haka dole ne farashi ya sauko. Mutanen kasashen waje sun gwammace su karya farashi su kwashi abun da suka iya samu su yi gaba.

Ga karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Shin me ya haddasa faduwar kasuwar hannun jari a Najeriya - 3' 07"