Masu salon magana na cewa, zo mu zauna zo mu bata. Wannan karin magana na iya tasiri a kowane irin al’amari na mu’amalar bil’adama. Saboda abu ne sannane samun sabanin fahimta tsakanin mutane daga lokaci zuwa lokaci, kamar yadda kuma akan samu daidaito bayan batawa ko kuma sabanin a tsakanin su.
Rumfar Jam’iyyar siyasa na daya daga cikin rumfunan dake tattaro mutane masu mabanbantan jinsi, dabi’a, shekaru, addini da kuma larduna.
Sai dai duk da haka, bakinsu kan zo wuri guda akan bantun akida da manufofin Jam’iyyar.
Jam’iyyar APC wadda aka kafa a shekara ta 2014 ita ce ke da gwamnatin tarayya a Najeriya da kuma kimanin gwamnoni 22 baya ga rinjaye a majalisar wakilai da ta dattawan kasar.
Wannan tagomashi ya biyo bayan nasarar da jam’iyyar ta samu ne a babban zaben kasar na shekara 2015 bayan da ta kada jam’iyya mai mulki a wancan lokaci wato PDP.
Gabanin haka, jimullar jam’iyyu uku ne suka hade suka zama ita APC, wato Jam’iyyar ACN, ANPP da kuma jam’iyyar CPC ta shugaba Muhammadu Buhari dake kan zango na biyu kuma na karshe na shugabancin Najeriya.
Sai dai, kasa da watanni 24 wa’adin karshe na shugaba Buhari da galibin gwamnonin jam’iyyar ya kare, rigingimu a cikin jam’iyyar a matakai daban-daban a kuma jihohin daban-daban na ci gaba wakana.
Hakan na zuwa ne, kasa da shekara guda da warware guguwar data sabbaba saukar shugaban ta na kasa Mr. Adams Oshiomhole wadda ya kai ga rusa shugabancin jam’iyyar na kasa dana jihohi tare da mika ragamar ta ga kwamitocin riko.
A can kololuwar jam’iyyar, masu lura da al’amuran jam’iyyar na ikirarin cewa, shugaba Buhari da babban jagora a jam’iyyar, tsohon gwamnan Legas, Ahmed Bola Tinubu, ba sa dasawa kamar yadda suke a da.
Rahotanni da dama sun ruwaito cewa, an jima rabon da a ga Tinubun a fadar shugaban kasar.
Sannan a baya-bayan nan, ba a ga shi Tinubun ba, a lokacin da Buhari ya kai ziyara a Legas a makon da ya shude.
Dadin dadawa, yayin wata hira da gidan talabjin na Arise TV, a lokacin da ya kai ziyarar ta sa a birnin na Iko, shugaban na Najeriya ya yi wasu kalamai da ake ganin na gugar zana ne.
“Duk wata shawara da jam’iyyar za ta yanke, sai an tuntubi dukkan mambobin jam’iyyar daga sama zuwa kasa, ba wai wani ne da ke zaune a Legas zai yanke mana shawara ba.”
Da yawa sun fassara cewa, da Tinubu Buhari yake wadannan kalaman, ko da yake fadar shugaban kasar ta yi maza ta ce an yi wa kalaman na Buhari mummunar fahimta.
“Fadar shugaban kasa na nesanta Buhari daga yunkurin da wasu ke yi na ganin sun hada fada tsakaninsa da babban abokin alaka, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.” In ji kakakin Buhari, Malam Garba Shehu.
Cin karo da bukatun juna na kusa dana nesa da wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar ta APC da Mr. Oshiomhole na daga cikin dalilan da suka tilasta masa barin shugabancin Jam’iyyar. Kazalika, irin wannan bukatu na taka rawar rikicin cikin gida tsakanin gwamnonin da wasu ‘yayan jam’iyyar ta APC a jihohinsu.
Misalin irin wannan rikici tsakanin gwamnan Jigawa da dan majalisar wakilan Najeriya Hon. Mohammed Gudaji ya sanya reshen karamar hukumar Kazaure na jam’iyyar dakatar da dan majalisar a watan jiya.
Makamancin wannan al’amari ya faru tsakanin gwamna Abdullahi Ganduje da dan majalisar wakilai Sha’aban Sharada, inda APCn ta dakatar da dan majalisar na tsawon watanni 12, kamar yadda takaddamar ra’ayi tsakanin masu neman takakarar gwamnan Kano a shekara ta 2023 ya sabbaba korar na hannun damar shugaba Muhammadu Buhari Abdulmajid Danbilki Kwamanda.
Sabanin bukata da gwamna akan zaben kananan hukumomi da za’a gudanar a jihar Jiagwa a Asabar ta mako mai zuwa, shi ne dalilan dakatar da Hon. Mohammed Gudaji, kamar yadda zaben kananan hukumomi da hukumar zaben Kano ta yi a cikin watan Janairun bana, shi ne silar kama wutar rigima tsakanin Hon. Sharada da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, al’amarin da ya kai ga jam’iyyar ta APC ta shelanta dakatar da dan majalisar a makon jiya.
Ko da yake, a nasu bangaren, shugabannin jam’iyyar reshen Kazaure da kuma Birnin Kano sun ce laifin kokarin zagon kasa ga jam’iyya da kokarin wargaza kan ‘yayanta kana da rashin mutunta shugabanni da dattawan jam’iyya na daga cikin dalilan dakatar da ‘yan Majalisar biyu, amma su kuma ‘yan majalisar sun musanta ikirarin, suna masu bayyana matakin dakatarwar a matsayin maras tasiri.
Yayin da Hon. Mohammed Gudaji da Hon. Sha’aban Sharada ke fadin haka, shi kuwa Abdulmajid Danbilki Kwamanda na cewa ya tsaga jam’iyyar ne, yana mai cewa, shi da abokan burmunsa sun kafa abin da suka kira APC akida tare da shan alwashin ci gaba da gwagwarmaya.
Sai dai Sanata Masa’udu El-Jibril Doguwa, tsohon wakilin Kano ta kudu a majalisar Dattawan Najeriya, ya ce son zuciya shi ke kawo irin wannan yanayi na kori in kora tsakanin ‘yan siyasa a wannan zamani.
“Kasuwar bukata ce kawai kuma ba da gaske ake ba. Duk lokacin da ka ga ‘yan siyasar yanzu na yin wasan kori in kora a wannan siyasar ta yanzu kasuwar bukata ce kawai ta taso, don haka suke amfani da makamin korar juna”
A cewar tsohon dan majalisar dattawan, a tsari na dokoki da ka’idoji da kundin tsarin mulkin jam’iyyu ya shimfida, akwai wasu rukunin ‘yan jam’iyya da ba sa dakatuwa haka kawai, ma’ana dokokin jam’iyya sun gindaya tsauraran ka’idojin kafin a kai ga matsayin dakatarwa ballantana korar su daga jam’iyya.
“Wadannan mutane sun hada da dan kwamitin koli na zartarwa na jam’iyya da shugaban jam’iyya na jiha da dan majalisar dattawa dana wakilai. Kazalika, ba’a iya dakatar da shugaban jam’iyya na mazaba sai a matakin karamar hukuma, yayin da kwamitin zartarwa na jiha ne kawai ke iya dakatar da shugaban jam’iyya na karamar hukuma, shi kuwa na jiha ana daukar matakin ladaftar da shi ne a kwamitin koli na kasa.”
Sai dai duk da haka, Sanata El-Jibril Doguwa ya yi ammana cewa, yanayin kori in kora a cikin jam’iyya babbar barazana ce ga makomarta.
Rikichin cikin gidan jamiyyar APC a Jihar Kaduna, shi ma ya yi sanadin kore-koren juna a Kananan hukumomin Kudan, Sabon gari, Soba, Kubau da kuma Zariya.
Da yake tsokaci kan wannan al'amari masanin kimiyyar siyasa kuma Malami a kwalejin share fagen shiga Jami’a ta Kano, Malam Kabiru Sa’idu Sufi, ya ce, dabi’ar korin in kora da ta kunno kai a cikin jam’iyyar APC na alamta yadda wasu suka jefa jam’iyyar a aljihunsu kuma hakan na tabbatar da rashin tafiya kafada da kafada tsakanin matakan shugabanci na jam’iyyar.
“Rashin tabbataccen kwamitin dattawa a APC da dabi’ar da akan shugaba Buhari da ita ta rashin tsawatarwa a yayin da ‘yayan Jam’iyyar sa ke rikici da juna na taka muhimmiyar rawa wajen faruwar irin wannan yanayi na kori in kora daya kunno kai cikin jam’iyyar APC kuma baa bin mamaki ba ne idan ya bazu zuwa wasu sassan kasar”
Kazalika, masanin kimiyyar siyasa kuma mai sharhi a fagen siyasar Najeriya ya ce rikicin dake wakana a tsakanin wasu gwamnonin na APC da ‘yan jam’iyyar a jihohinsu, al’amari ne dake nuna cewa, za’a ja layi tsakanin fadar shugaban kasa da gwamnonin akan wasu batutuwa da za su taso nan gaba masu nasaba da kakar zaben shekara ta 2023.
“Idan ka lura sosai za ka ga cewa, wannan rikicin dakatarwa ko kori in kora a APCn Kano da Jigawa ya shafi wasu mutane ne na hannun damar shugaban kasa (Hon. Mohammed Gudaji, Hon. Sha’aban Sharada da kuma Abdulmajid Danbilki Kwamanda) kuma biyu daga cikin su, ‘yayan tsohuwar jam’iyyarsa ne ta CPC.
Haka kuma, galibin gwamnonin nan na jam’iyyar APC na kan wa’adinsu na karshe ne kuma suna da bukatun siyasa na zama wani abu a gaba kuma ba lallai ya yi daidai da muradu ko ra’ayin fadar shugaban kasa ba”
A cewar Malam Kabiru Sa’idu Sufi, wadannan dama kasancewar, shi ma kansa shugaba Buharin na zangon karshe da kuma wasu al’amura na rashin hadin kai tsakanin jam’iyyar da kuma tasirin gidajen gyauron tsaffin jam’iyyun da suka rikide suka zama APC (ACN, ANPP, CPC) kana da yanayin zafin bukata a zukatan ‘yan siyasar Najeriya, abubuwa ne da za su ci gaba da kasancewa babban kalubale ga jam’iyyar ta APC daga nan zuwa zaben shekara ta 2023.