An gano wannan badakalar ne a cikin wani rahoton binciken kudin da ya yi nuni da yadda shugabancin zauren majalisun tarayyar kasar biyu suka kashe naira biliyan uku a majalisar dattawa baya ga wasu naira biliyan 5 da miliyan 500 a majalisar wakilan kasar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Haka kuma rahoton binciken ya yi nuni da cewa a shekarar 2019 ne majalisun tarayyar Najeriyar, suka kashe kuddadden ba tare da shaidar yadda aka kashe su ba.
Kazalika, rahoton da Aghughu Adolphus dake zama mai binciken kudin na Najeriya, ya fitar ya lissafa majalisar dattawa, majalisar wakilai da hukumar kula da harkokin majalisar dokoki ta kasa a cikin wadanda ake zargi da kashe kudaden ba bisa ka’ida ba.
Rahoton da Aghughu Adolphus ya gabatar wa akawun majalisar a watan agusta ya ce an kashe kudaden ne a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2018 ba tare da cike takardun da suka dace ababen da aka yi da kudadden ba.
A cewar Aghughu Adolphus, a cikin shekarar da ta gabata ne kwamitin kudaden gwamnati na majalisun kasar ya kaddamar da bincike kan hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya daga shekarar 2015 zuwa 2018.
A nasa bayani shugaban cibiyar bin diddigi da tabbatar da gaskiya a harkokin majalisa wato CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce jin sakamakon binciken na tada hankali kuma abin takaici ne a kashe kudadden gwamnati ba bisa ka’ida ba.
Akawun majalisar tarayya, Austen Adesoro, a yayin mayar da martani ya bayyana cewa wannan batun ya shafi shekarar 2019 ne kawai kuma tuni aka shawo kansu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake gano badakalar kudi a ma’aikatu ko hukumomin gwamnatin tarayya ba lamarin da masana abun duba wa ne don tattalin arzikin kasa na kara shigan matsin tattalin arziki.