Chris Spear na da matukar sha’awa a fannin dafa abinci. Tun yana da shekaru 16 da haihuwa ya fara dafa abinci na kwararru. A shekarun da suka gabata ya yi aiki a gidajen saida abinci har ta kai ga yana da mutane kusan 100 dake aiki a karkashin sa. A lokacin ne ya fara tunanni yana son ‘yancin kansa yana kuma so yayi na shi kirkire-kirkiren. Don haka sai ya daina aiki a gidanjen saida abincin ya fito da nasa kamfanin abincin, mai suna Perfect Little Bites.
“Yin sana’a ba abu bace mai sauki, amma ina son in sami lokacin kaina, lokacin iyali na ko kuma in zauna gida in dafa ma wani abinci. Ina so in sami abinda zan bugi kirji in ce nawa ne,” a cewar Mr. Spear.
Mr. Spear, ya kan kwashe sa’o’i yana aikin dafa abinci amma baya gajiya. Kodayake wani lokaci yakan damu akan cewa zama kwararren mai dafa abinci zai iya kawo mashi kadaici. Amma wannan ya tsuma shi har ya ga kirkiro wata kungiya a shafin yanar gizo mai suna Chefs Without Kitchen, don masu dafa abinci.
Tun bayan da kungiyar ta kafu a watan Janairun da ya gabata, masu dafa abinci kusan 100 suka shiga.