Shettima Ya Yabawa Ziyarar Sabon Sifeton ‘Yan Sandan Najeriya Zuwa Jihar Borno

Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima

Bayan kara samun kwanciyar hankalin da ake dada samu a jihar Borno da ma Arewa maso Gabashin Najeriya, jami’an tsaro na ta karawa al’ummar yankin kwarin gwiwa ta hanyar yawan kai ziyara don tabbatar da zaman lafiya yadore.

Sabon shugaban ‘yan sanda na Najeriya ya ziyarci jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, wanda yace ya je ne domin ganin ta inda zai karawa rundunar su ta can karfi saboda inganta maganar tsaro da aiki tukuru.

Babban Sifeto Idris Abdullahi ya bayyana cewa, jihar Borno waje ne da yayi ai shekaru 5 a garin. Inda ya taho da tawagarsa har da ma shugaban hukumar jami’an gidan yari wato Ganduroba, da kuma jami’an kiwon lafiya.

Gwaman jihar Borno Kashim Shettima ya bayyana jin dadinsa game da ziyarar da aka kawo musu maimakon yadda wasu ke shantakewa a birnin tarayyar kasar wato Abuja, su dinga surutai maimakon tasowa su taimakawa garin na Borno.

A yayin ziyarar ne kuma sai wakilinmu Haruna Dauda Biu ya tattauna da Sifeton ‘Yan Sandan don jin karin dalilansa na ziyarar da ya kai jihar. Musamman ma da yake ya kwashi tawaga da dama tare da shi da suka raka shi.

Your browser doesn’t support HTML5

Shettima Ya Yabawa Ziyarar Sabon Sifeton ‘Yan Sandan Najeriya Zuwa Jihar Borno - 4'46"