Shettima Ya Dawo Daga Taron Majalisar Dinkin Duniya

Lokacin da mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya sauka a Abuja bayan kammala halartar taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, Amurka. (Hoto: Facebook/Stanley Nkwocha)

Shettima ya wakilci Shugaba Bola Tinubu ne a taron wanda aka yi a karo na 79 a birnin New York da ke Amurka.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya dawo Najeriya bayan halartar taron Majalisar Dinkin Duniya a New York da ke Amurka.

An kwashe kwanaki hudu ana taron wanda ya tattaro shugabannin kasashen duniya tun daga ranar 24 zuwa 28 ga watan Satumba.

Shettima ya wakilci Shugaba Bola Tinubu ne a taron wanda aka yi a karo na 79.

“A yau, (Lahadi) na dawo Abuja bayan nasarar wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 da aka kammala a birnin New York, Amurka.

“Yayin da nake a New York, na gabatar, a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jawabin kasa na Najeriya a lokacin muhawarar.” Shettima ya ce cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta a ranar Lahadi.

“Shettima zai hadu da Shugaba Bpla Ahmed Tinubu don gudanar da bikin cikar Najeriya sheakru 64 da samun ‘yancin kai.” Kakakin Tinubu na musamman Stanley Nkwocha ya ce cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.