WASHINGTON DC - An wallafa sunan Simon Ekpa a jerin sunayen mutanen da hukumomin sojan Najeriya ke nema tare da wasu mutum 96 suka fito daga sassan kasar daban-daban.
A jikin wani kwali me dauke da hotunan mutanen da ake tuhuma, shelkwatar tsaron tace ta ayyana sunayen mutane 97 da take nema ruwa a jallo saboda laifuffukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi da barazanar ballewa daga najeriya.
Mafi shura a cikin mutanen da ake nema shine simon ekpa wanda ke iko da wani tsagi na haramtacciyar kungiyar fafutukar kafa kasar biafara ta ipob wanda kuma aka dorawa alhakin ayyana dokar nan ta zaman gida tilas a duk litinin a yankin kudu maso gabashin najeriya.
Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba, ya tabbatar da sunaye da hotunan mutanen da aka ayyana nemansu.
Mutanen da ake neman da suka hada da; kwamandojin 'yan ta'adda da 'yan bindiga da masu tada kayar baya sun fito ne daga shiyoyin arewa maso gabas da arewa maso yamma da arewa ta tsakiya da kuma kudu maso gabashin najeriya.
A jikin kwalin dake dauke da hotuna da sunayen mutane 97 da ake neman an bada bayanin shiyoyin da suka fito.
Bayanin ya bayyana cewar mutane 43 daga cikin sunayen da ake neman sun fito ne daga shiyar arewa maso yamma dake fama da matsalar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun hada da jagororinsu irinsu Alhaji Shingi da Malindi Yakubu da Boka da Dogo Gide da Halilu Sububu da Ado Aliero da Bello Turji da Dan Bokkolo da Labi Yadi da Nagala da Sa'idu Idris da Kachalla Rugga da Sani Gurgu.
A shiyar arewa maso gabas kuwa kwamandojin 'yan ta'addar da aka ayyana nemansu ruwa a jallo sun hada da; Abu Zaida da Modu Sullum da Baba Data da Ahmad da Sani Teacher da Baa Sadiq da Abdul Saad da Kaka Abi da Muhammad Khalifa da Umar Tella da Abu Mujahid da Malam Muhammad da Malam Dahiru Baga da Uzaiya da kuma Ali Ngule.
A shiyoyin arewa ta tsakiya da kudu maso gabashin Najeriya kuma an ayyana neman 'yan bindiga da masu tada kayar baya da gaggan masu laifi 21 ruwa a jallo.
Mutanen sun hada da jagoran wani tsagi na kungiyar 'yan awaren Biafra, Simon Ekpa da Chika Edoziem da Egede da Zuma da Thankgod Gentle da Flavor da Mathew da David Ndubuisi da High Chief Williams Agbor da Ebuka Nwaka da kuma Friday Ojimka.
Sauran 'yan ta'addar da suka fito daga shiyar kudu maso gabashin Najeriya sun hada da; Obeimisi Chukwudi da aka fi Sani da Dan Chuk da David Ezekwem Chidiebube da kuma Amobi Chinonso Okafor da aka fi Sani da Temple.