Sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, y ace shelkwatar sojojin kasar dake Abuja, babban birnin kasar, za ta yi kaura zuwa Maiduguri domin a kawo karshen matsalar Bok Haram
Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabinsa na farko a dandalin Eagle Square bayan da ya karbi ragamar mulki a matsayin sabon shugaban Najeriya.
Najeriya, musamman ma a yankin arewa maso gabashin kasar, ta kwashe kusan shekaru shida tana fama da matsalar hare-haren kungiyar Boko Haram, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane kana sama da miliyan suka bar muhallansu.
Daga cikin babban al’marin da ya ja hankulan kasashen duniya game da matsalar ta Boko Haram, shi ne sace ‘yan makaranta Chibok da ‘yan kungiyar Suka yi a watan Aprilun bara, lamarin aka yi Allah wadai da shi a duk fadin duniya.
Har ya zuwa yanzu, ba a san inda wadannan ‘yan mata su 219 su ke ba yayin da rundunar sojin kasar ta bayyana kubutar da wasu mata da ‘yan mata da dama a farkon watannan.
Matsalar tsaro na daga cikin matsalolin da ‘yan Najeriya suka zuba ido su ga ko gwamnatin ta Buhari za ta iya magancewa yayin da matsalolin rashin aikin yi da wutar lantarki da kuma cin hanci da rashawa suka dabaibaiye kasar.
Ga karin bayani a tattaunawarmu da Nasiru Adamu El-hikaya a dandalin VOA:
Your browser doesn’t support HTML5