Shekaru 17 Tana Dauke Da Cutar Kanjamau

Hukumar lafiya ta duniya ta ware 1 ga Disamban kowacce shekara a matsayin ranar wayar da kan al’umma kan cuta mai karya garkuwar jiki.

A wani bincike da hukumar ta fitar ya bayyana cewa , matasa tsakanin shekara 10 zuwa 19 na dauke da cuta mai karya garkuwar jiki ba tare da samun kulawar da ya dace ba.

Rahoton ya kuma kara da cewa, kimanin miliyoyin matasa na da yiwuwar kamuwa da cutar, binciken ya kuma ce rashin kulawar ga wadanan matasa na haddasa karuwar cutar da kimanin kashi 50 cikin dari daga tsakanin 2005 zuwa 2012.

Rahoton ya kara da cewa kimanin mutane miliyan 35 ke dauke da cuta mai karya garkuwa a duk fadin duniya

Taken ranar a bana kuwa shine’ tabbatar da an kawar da cutar mai karya jiki kaf’