Shekara Daya Da Sace Daliban Chibok

'Yan matan Chibok da suka tsallake rijiya da baya

Ranar 14 ga watan Afirilun shekarar 2014 'yan kungiyar Boko Haram suka kai samamme a makarantar 'yan mata dake Chibok jihar Borno inda suka sace dalibai 279 kafin wasu su samu su kubuce.

'Yan gwagwarmayar dawo da 'yan matan Chibok sun yi caji domin gagarumin nuna juyayin shakara daya da sace matan kuma har yanzu ba'a kai ga nasarar samosu ba.

Jagorar masu gwagwarmayar Obi Ezekiesilieze bata iya mallakar zuciyarta ba inda ta zubar da hawayen juyayi da lasar takobin cewa ba zasu daina ba sai matan sun dawo. Dr Emma Shehu shi ne jami'in labarun gwagwarmayar. Yace sun gane cewa jami'an gwamnati basu san inda 'yan matan suke ba sai karerayi suke ta gindiyawa. Saboda haka sun nace sai an nemo 'yan matan.

Zabiyar gangamin Aishatu Yusuf na ganin domin 'ya'yan talakawa aka sace shi ya sa har yanzu ba'a gano su ba. Tace ai da aka sace kawun shugaban kasa an dawo dashi. Lokacin da aka sace uwar Ngozi Iweala nan da nan aka kwatota.Dole kasar ta tashi ta kare kowa ko yana da kudi ko bashi da shi. Gwamnatin kasar ta daina nuna banbancin bangaranci ko na addini ko na arziki.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shekara Daya Da Sace Daliban Chibok - 3' 02"