Sheikh Ahmed Al Tayeb Ya Nemi A Yiwa Manhajar Koyas da Addinin Musulunci Garanbawul

Sheikh Ahmad Al Tayeb a dama yana shan hannu da shugaban Hamas

Sheikh Al Tayeb ya nemi a yiwa manhajan koyas da musulunci garambawul a jami'o'i da sauran makarantun nazarin addinin musulunci.

Sheikh Ahmad Al Tayeb ya bada shawarar ce a matsayin matakin magance gurguwar fahimta da wasu musulmi ke yiwa Kur'ani da koyas war Annabi Muhammada (S.A.W.).

Dr Aliyu Bashir Umar babban limamin masallacin Juma'a na Alfaqana a Kano kuma mataimakin shugaban kungiyar malaman addinin musulunci ta Afirka mai kula da shiyar Afirka ta Yamma yace manhajar da ake anfani da ita bata da wata masala.Yace duk yawancin wadanda suka kafa kungiyoyi ta'adanci ba malaman addinin Islama ba ne. Wanda ya kafa kungiyar al-Qaida Usama Bin Laden ilimin tsimi da tanadi ya koya wato economics.Shukuri Mustapha injiniya ne. Al-Zawahiri likita ne. Wadanda suke da ilimin addini da suka shiga ta'adanci Taliban ne kuma su din 'yan leken asirin kasar Pakistan da Saudiya ne suka hade. Kungiyar ISIS ma wasu gwamnatoci ta hanyar leken asiri suka kafata.

Galibin kungiyoyin addinin musulunci masu tsatsauran ra'ayi 'yan boko ne suke kafa su. Dr Aliyu Umar ya bayyana abun da ya sa hakan ke faruwa. Yace 'yan boko suna da wayewa ta zamani saboda tarbiyar addini da son addinin suka ga yadda addinin musulunci yayi na kawo canji a cikin al'umma. Sai suga to ai maimakon su je su dauko aikdar gurguzu ko akidar kishin kasa ga akida ta musulunci. To amma saboda nisansu da ilimin addini da kuma nisansu daga malamai sai suka samu gurbatacciyar fahimta. Shi ne ya kaisu ga kama ta'adanci su dauka abun da suke yi jihadi ne. Da zasu koma wajen malamai zasu fada masu yadda jihadi yake cikin addinin musulunci. Suna sanya fahimtarsu a gaba kana su lankwaso Kur'ani domin su karfafa fahimtarsu.

Shi ma Sheikh Ibrahim Khalil masharurin malami a Kano yayi tsokaci akan batun neman a gyara manhajar. Yace ba za'a ce Al Tayeb yayi kuskure ba domin kowa ya san jami'ar Al Azar tana bin masakaicin ra'ayi da kuma kokarin daidaita alamura.Ba magana ce ta manhaja ba. Magana ce ta cewa malamai da suke koyas da addini su zama masu sassaucin ra'ayi. Malamai masu matsakaicin ra'ayi su ne suke da daman fahimtar da mutane fiye da masu tsatsauran ra'ayi.Mutane su gane cewa fahimta ba daya ba ce. Fahimta tana da yawa.Akwai wasu kasashe akan fahimta daya suke koyas da addinin musulunci. Masu matsakaicin ra'ayi su ne ya kamata su dinga yada addinin. Malamai masu tsatsauran ra'ayi yakamata ana taka masu birki lokaci lokaci.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Sheikh Ahmed Al Tayeb Ya Nemi A Yiwa Manhajar Koyas da Addinin Musulunci Garanbawul - 3' 31"