Shayar Da Nono Nada Mahimmaci Ga Jarirai

Jariri

A yau ne aka shiga makon sayar da nonon uwa zalla,hukumar lafiya ta duniya dai ce ta ware wannan ranar shekaru 25 da suka wuce wanda taken makon na bana, tabbatar da an jure wajen shayar da nonon uwa ga jariri.

Wata mai shayarwa Maryam lawan Imam ta bayyana mana dalilan da ya sa take shayar da danta nono zalla da irin alfanun da hakan ke tattare da shi ga jarirai dama ita mahaifiyar kanta.

Ko da yake a haihuwarta ta biyu da jarirar ta kai watannin hudu sai ta daina kama nono- aka kuma fara bata ruwa da madara ko menene dalilin.

Akan haka ne muka zanta da wata ma’aikaciyar kiwon lafiya a asibitin malam Aminu Kano, a bangaren yara Malama Hadiza Abdulmalik, ta bayyana alfanun da ke tattare da bada nonon uwa zalla da kuma muhimmancin shayar da nono akan kari.

Hadiza dai ta ja hankali iyaye mata da su daure wajen shayar da nono akalla na fiye da shekara tare da tsaftace abinci ko abin shan jariri.

Your browser doesn’t support HTML5

Shayar Da Nono Nada Mahimmaci Ga Jarirai - 5'34"