Shawarwari Kan Abinci Mai Lafiya Lokacin Azumi

A yau mun sami zantawa da wata jami’a mai kula da ingantattun abinci a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano malama Halima Musa Yakasai – inda ta yi mana bayani dangane da ire-iren abincin da ke bata ciki a lokacin azumi.

Ta ce cin abinci mai sanyi da yawa sosai na bata ciki ko, ko wasu nau’ukan abinci da ake cin su da zafi sosai na bata ciki ko yanayin yadda mata ke miya wajen dafa ganye ya nuna lugub duk an kashe abubuwan dake sa lafiya cikin abincin na daga cikin abubuwan da ke bata ciki.

Malamar ta kara da cewa yana da kyau mace ta wanke ganyen da za’a yi afani da shi sosai ta hanyar sanya gishiri wajen wanke shi, tare da jan hankalin mata da su lura da wasu tsutsotsi da kasa a cikinsu.

Ta ce a bangaren kayan marmari akwai wasu da kan haddasa bacin ciki, misali idan aka sha mangwaro da yawa na bata ciki- ta kara cewa yana da kyau su ma kayan marmarin a wanke su sosai.

Ta ce a ka’ida kamata ya yi kowanne mutum ya sha lemo guda biyu, haka nan kankana ba’a so a sha ta da yawa, inda ta ce ya kamata a ci wadannan abubuwa a cikin hankali ba tare da hadama ba.

Daga nan kuma mun sami zantawa da wasu da suka sami damar karbar abinci sadaka da gwamnatin jihar kano ke rabawa a duk watan ramadana sun ce wasu lokutan abincin na isa wasu lokutan.

ku biyu domin jin cikakkiyar hirar.

Your browser doesn’t support HTML5

Shawarwari Kan Abinci Mai Lafiya Lokaci Azumi