Missalan irin shari’un da yanzu aka kammala sun hada da na gwaman Wike na Rivers, da yayi nasara kan ‘dan takarar APC Dakuku Peterside sai Benue Samuel Otom yayi nasara da Dankwambo a Gombe, abinda ba a gani ba shine shari’un sun tabbatarwa gwamnoni ne nasara, inda zuwa yanzu ba a sami dan takara ba da ya amshe kujerar gwamna ba.
Adamu Chilariye, shine shugaban APC na Yobe da ya shaida yanke wannan hukuncin da ya basu nasara, inda ya tabbatar da cewa sun sha wahala, kuma Adamu Maina Waziri yasan cewa dama can bai ci zabe ba. kuma ya nuna jin dadin wannan nasara da suka samu daga kotun koli.
Su ma a bangaren su mukarraban Adamu Maina Waziri kan wannan hukunci sun bayyana ra’ayinsu, Hassan Gimba wanda yake kakakin ‘dan takarar na PDP, yace yanzu haka akwai sauran kara akan rantsuwa sau uku, wanda ake kalubalentar gwamnan Yobe, inda tun lokacin Shugaba Jonathan akayi ta cece kuce akan maganar.
Yanzu dai shari’ar da ake dokin sanin hukuncin da za a yanke itace ta gwamna Darius Ishaku na Taraba da ‘yar takara mace tilo Hajiya Jummai Alhassan ta APC.
Your browser doesn’t support HTML5