Shari'ar Carlos The Jackal

  • Ibrahim Garba

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da kasarsa ke wa Carlos The Jackal Shari'a

Dan ta’addan nan da ya yi kaurin suna, wanda kuma aka samu

Dan ta’addan nan da ya yi kaurin suna, wanda kuma aka samu da laifi, wanda aka fi sani da suna Carlos the Jackal, zai fuskanci shari’a a yau Litini a birnin Paris sabado zargin taka rawa a jerin hare-haren ta’addanci a kasar Faransa a farkon shekarun 1980 zuwa sama.

Hare haren da aka kai kan jiragen kasa biyu da wani ofishin jarida a cikin 1982 da 1983 sun hallaka mutane 11 tare da raunata 140. Za a kuma yi shari’a wa wasu mutane uku da ake zarge da hada kai da shi duk kuwa da ba su hannu.

Masu gabatar da kara sun ce sun bankado abin das u ka ce hujjoji ne na laifukan Carlos a cikin wasu takardun tarihi na ‘yan gurguzu a Hungary da kuma tsohuwar Jamus ta Gabas. Carlos dai ya ce shi bai aikata wani laifi ba.

Da ma yana daurin rai da rai ne saboda ne saboda kashe wasu jami’an ‘yan sanda biyu da wani mai bayar da bayanan sirri a 1975.