Sharhin Muryar Amurka: Kira Kan Kare Hakkokin Bil'adama da Tabbatar Da Tsaro A Kenya

KENYA-POLITICS-UNREST-DEMONSTRATION

Amurka na neman a tabbatar da kariya da tsaro a Kenya. An gudanar da gagarumar zanga-zanga a babban birnin Nairobi bayan da aka gabatar da kudirin dokar kudi da zata sa a kara haraji a kasar. 

An sami sahihan "rahotannin cin zarafin masu zanga-zangar," a cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller a yayin wani taron manema labarai. Amurka ta yi kira ga gwamnatin Kenya da ta yi amfani da matakai amma ba masu zafi ba da hana cutar da farar hula wajen tunkarar masu zanga-zangar lumana.

“A saboda haka, muna Allah wadai da tashin hankalin da aka yi a lokacin zanga-zangar da aka yi a Nairobi da kuma kewayen Kenya. Muna jimamin rayukan da aka rasa da wadanda suka jikkata muna kuma yi wa iyalan wadanda abin ya shafa ta'aziyya. Muna yin kiran a maido da doka da oda da samar da damar tattaunawa."

Tuni dai shugaban kasar Kenya William Ruto ya janye dokar harajin. A wata rubutacciyar sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fitar, ya godewa shugaba Ruto bisa daukar matakan rage zaman dar dar da kuma yin alkawarin fara tattaunawa da masu zanga-zangar da kungiyoyin farar hula. Sakatare Blinken ya jaddada mahimmancin jami’an tsaro su kaucewa cin zarafin jama’a da kuma karfafa gudanar da bincike cikin gaggawa kan zarge-zargen cin zarafin bil’adama.

Haka kuma, Kenya ta taka rawar gani wajen ba da gudummawa a rundunar wanzar da zaman lafiya ta Kasa da Kasa da nufin maido da tsaro da wadata a Haiti. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Miller ya jaddada cewa, ya kamata dukkan ma'aikata, ciki har da daga Kenya da sauran kasashe su sami horo mai zurfi kan kare hakkin dan adam kafin a turasu aiki wani wuri.

Amurka na aiki tare da Kenya da sauran abokan hulda don sanya batun "daukar muhimman matakan sa ido don hanawa, da bincike, da magance lamari, da kuma bayar da rahoto kan duk wani cin zarafi ko muzanta hakkin dan adam da ke da alaka da Ofishin MSS," a cewar Miller.

“Za mu ci gaba da yin aiki tare da bincikar ma’aikatan da za a tura aiki, saboda akwai muhimmanci a mutunta ’yancin mutanen Haiti a yayin kokarin maido da doka da oda da za'a yi."

Amurka ta kuduri aniyar yin aiki kafada da kafada da gwamnati da jama'ar Kenya yayin da suke kokarin magance kalubalen tattalin arzikinsu, suna kuma kokarin ganin an tabbatar da kare hakkin bil'adama a Kenya da ma duniya baki daya.