SHARHIN MURYAR AMURKA: Amurka Zata Ba Da Tukuicin Dala Miliyan 5 Ga Duk Mai Bayani Kan Shugaban ISIS Abu Ali Al-Tunisi

RFJ al-Tunisi

Gwamnatin Amurka ta yi tayin ba da tukuicin dala har miliyan 5 ga duk wanda ke da bayanan da za su sa a gano Abu Ali al-Tunisi ko kuma inda yake. Al-Tunisi jigo ne a kungiyar ta'addanci ta ISIS. Yana da rauni a hannunsa na dama da idon dama.

Al-Tunisi shi ne shugaban da ke kula da harkokin sarrafa abubuwa a kungiyar ISIS a Iraki. Ya horar da ‘yan kungiyar ISIS kan yadda ake hada ababen fashewa, da rigunan da ake makalawa bam don masu kunar bakin wake, da bama-bamai. Haka kuma Al-Tunisi ya ba da horo mai zurfi kan kera makamai da kuma makaman guba.

An ayyana ISIS a matsayin kungiyar ta'addanci ta kasashen waje tun a watan Disamba na 2004 a karkashin sashe na 219 na dokar shige da fice ta Amurka. A cewar Rahoton ma’aikatar harkokin waje na shakarar 2022 game da ta’addanci, ISIS ta "fadada ayyukanta da daukar mayaka a cikin manyan yankuna, inda kungiyar ta fadada rassa da kungiyoyin da take alaka da su a fadin duniya zuwa kusan akalla 20." Amurka ta kasance kasar kawance da kungiyar hadin kai don yaki da ISIS ta Duniya, wacce Amurkar ta kafa a 2014.

"Hadin kan Kungiyar hadin kan yaki da ISIS ta duniya na nan daram, kungiyar ta kuma kuduri aniyar tabbatar da jurewa wajen murkushe ISIS a duk inda kungiyar ta yi yunkurin gudanar da ayyukanta, da kuma hukunta 'yan ta'addar ISIS a karkashin tsarin shari'ar manyan laifuka," a cewar wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar.

Idan kai ko wani wanda ka sani yana da bayani akan al-Tunisi ko inda yake, to a tuntubi shirin ba da tukuici na Rewards for Justice ta hanyar sadarwar sigina, Telegram, ko Whatsapp a lambar waya +1 202-702-7843, ko kuma ta shafin shirin na yanar gizo, a rewardsforjustice.net.

Za a yi bincike a kan duk rahotanni masu inganci da aka samu, kuma za a sakaya sunayen duk wadanda suka ba da bayanai.