Shahararren dan wasan fina-finai a Amurka, Chadwick Boseman ya mutu yana da shekaru 43.
WASHINGTON D.C —
Boseman, wanda shi ne jarumin fim din “Black Panter” da ya yi fice sosai, bai taba bayyana yanayin lafiyar jikinsa ba, to amma ya mutu ne sakamakon cutar sankara wato kansa, kamar yadda jami’insa na watsa labarai ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.
An gano yana da cutar ta sankara karon farko a shekara ta 2016, to amma Boseman ya ci gaba da mai da hankali akan harkokinsa na fina-finai a Hollywood.
Wata sanarwa da aka wallafa a shafukan sadarwar internet na marigayin, ta ce “ya rasu ne a gidansa, kusa da matarsa da sauran danginsa.”
Boseman shi ne dan wasan kwaikwayo bakar fata na farko da ya yi fim na kashin kan sa, wato fim din da ya yi fice sosai a shekarar 2018 mai suna “Black Panter.”