Dakta Uboh, wanda zai bayyana gaban kwamitin bahasi na bainar jama'a kan koke-koken jama'a ranar Laraba, ya ce ya na da kundi mai kusan shafi 1000 na shaidar batan kudin.
A baya, Dakta Uboh ya sha bankado irin wadannan bayanai har kotu ta taba tura shi zaman wakafi a gidan yarin Kuje, kan shari'ar bata suna ga gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele. Ya ce kudin sun shafi wasu manyan bankuna da daya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa da kuma wasu kamfanonin man fetur.
Daya daga cikin zarge-zargen ya shafi rashin shigar da zunzurutun kudi dala biliyan takwas daga kamfanonin mai a hukumar tara kudaden shiga, tun zamanin mulkin tsohon shugaban hukumar, Tunde Fowler.
Sai kuma zargin da ya shafi kamfanin sadarwa na MTN mallakin kasar Afirka ta Kudu, wanda ya ha'inci asusun ajiya na ketare na Najeriya na tsabar kudi sama da dala Biliyan 25.
A ra'ayin mai kwarmaton, matukar za a tsaya kan gano irin wadannan makudan kudade, Najeriya ba ta bukatar nemo lamuni daga ketare.
Mai taimaka ma Uboh ta fannin tafinta, Magaji Muhammad Yaya, ya yi karin bayani ta hanyar kira ga Shugaba Buhari da ya binciki zarge-zargen. Haka kuma ana sa ran duk wadanda a ke zargin, za su halarci zaman don kare kan su.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5