Fitaccen dan wasan damben na Amurka zai gana da Masoyansa, da ‘yan jarida, da kuma Ministan Wasannin Najeriya.
Floyd Mayweather ya isa Abuja, babban birnin Najeriya ne da yammacin ranar Lahadi inda ya gana da masu shirya wani wasa da za a yi wannan makon a Dubai.
Ya kira wani taron manema labarai tare da abokin karawarsa a wasan da ke tafe, wato Don Moore.
Mayweather ya ce zuwansa Najeriya na daga cikin shirye shiryensa na bunkasa wasan damben boxing a Afirka.
Ya fadi cewa su na aikin bude wuraren boxing na Mayweather a Najeriya. “Muna kuma son gina wasu cibiyoyin damben boxing don matasa da yara masu tasowa, a cewar Mayweather." Ya kuma ce, "za mu ci gaba da aiki tare da fatan wata rana za mu sami wani dan wasan kamar Floyd Mayweather daga Najeriya."
An dade ba a ba damben boksin muhimmanci a Najeriya sakamakon jan hankalin da wasanni, kamar kwallon kafa, ke kara yi. Ba a samar da kudade don gidajen damben boksin na jama'a a kasar, haka kuma ba a kula da su sosai.
Zakaran damben boksin na Najeriya, Olanrewaju Durodola, ya ce akwai bukatar hukumomi su shigo harkar, kuma ta yiwu ziyarar Mayweather ta kawo sauyi mai kyau a Afirka.