Shahararren Dan Jaridar Amurka Larry King Ya Rasu

Larry King

Larry King

Rahotannin sun nuna cewa cutar coronavirus ce ta yi sanadiyar mutuwar Larry King, wanda shirinsa na "Larry King Live" na gidan talabijin din CNN ya tattaro miliyoyin 'yan kallo daga fadin duniya.

Larry King, wanda ya yi wa gidan talabijin din CNN da wasu kafafen yada labarai hira da dubban shugabannin duniya, da ‘yan siyasa, da taurari a fannin nishadi a aikinsa da ya kwashe sama da shekara 60 ya na yi, ya rasu ya na da shekaru 87, a cewar gidan talabijin din CNN ranar Asabar 23 ga watan Janairu, gidan talabijin din ya ambaci wata majiya da ke kusa da iyalin King.

Da ma an kwantar da King asibiti a birnin Los Angeles saboda ya kamu da cutar COVID-19, a cewar kafafen yada labarai da yawa. Ya jure rashin lafiya sosai tsawon shekaru, ciki har da bugun jini a shekarar 2019 da kuma cutar suga. A asibitin Cedars Sinai da ke Los Angeles aka kwantar da shi sama da mako guda, a cewar CNN.

Miliyoyin mutane sun kalli hirarrakin da King ya yi da shugabannin duniya, da taurari a fannin nishadi a shirin CNN na “Larry King Live,” wanda aka fara daga shekarar 1985 zuwa 2010.

Jingine da teburinsa daga zaune, kuma sanye da riga mai dogon hannu da aka nannade da kuma tabarau, King ya sa shirinsa ya zama daya daga cikin shirye-shiryen da suka fi tattaro ‘yan kallo a CNN ta hirarrakinsa, da tattaunawar harkokin siyasa, da abubuwan da ke faruwa, muhawara da kuma hira ta wayar tarho.

Ko a lokacin da ya yi tashe, masu caccakar King sun zarge shi da gazawa wajen yin bincike sosai kafin ya yi hira da bakinsa kuma ya na yi musu tambayoyi masu sauki. Ya maida martini da cewa baya yin bincike sosai saboda ya na so ya karu tare da masu kallon shirinsa. Bayan haka, King ya ce, bai taba sha’awar a yi masa kallon dan jaridar ba.