Shagabar Hukumar Zaben Ghana Ta ce Sun Shirya Wa Babban Zaben Kasar

Jean Mensa Shugabar HUkumar Zaben Ghana

Yayin da ake shirin babban zaben kasar Ghana ranar Litinin 7 ga watan Disamba, shugabar hukumar zaben kasar ta ce hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zaben gaskiya da adalci.

A wata hira da wakilin Muryar Amurka Peter Clottey ne babbar lauyar kuma shugabar hukumar zaben Ghana Jean Adukwei Mensa ta bayyana cewa hukumar ta shirya gudanar da zaben.

Mensa ta ce tsarin gudanar da zaben kasar tsari ne bayyananne kuma a yanzu haka su na da kungiyoyi da ke sa ido kan zaben na cikin gida da na kasashen waje 28, bayan haka sun bai wa kafafen yada labarai kusan 10,000 takardar izinin bibiyar zaben a karon farko a tarihin zabukan kasar.

Kalaman na Mrs. Mensa na zuwa ne bayan ganawa da wakilai masu sa ido kan zaben na cikin gida da na waje a shelkwatar hukumar zaben kasar da ke Accra babban birnin kasar a jiya Juma’a. Mrs. Mensa ta bayyana wa wakilan ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu a shirin zaben na shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da za a yi ranar Litinin.

A halin da ake ciki, jami’an hukumar zaben kasar sun ba tsohuwar shugabar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf, wacce ke jagorantar tawagar wakilan sa ido a zaben daga ECOWAS, da tsohon shugaban Afirka ta Kudu Kgalema Motlanthe cikakken bayani aka nshirin zaben.