A kowanne irin abu da dan adam yake a rayuwa yana tattare da nashi irin kalu balen, a lokacin da nake jami'a kalubale da na fuskanta shine, na wasu malamai kan sanya darasi wanda baya cikin tsari manhaja da aka fitar dashi tun daga farko, inda a mafi yawan lokuta hakan kan shiga hakkin dalibai, a ta baki wata matashiya malama Baraka Salisu.
Kamar sauran matasa Baraka, bata fuskanci matsala ba a fanni neman gurbi na karatu, domin kuwa abinda take nema shi ta samu a jami'a, kuma ta kammala karatunta ne ba tare da ta samu wata matsala ba a fannin karatu ko daga wajen malamai.
Ku Duba Wannan Ma Ina Waka Ne Domin Fadakar Da Matasa Illar Kwaya: Aisha ArewaTa ce babba abin sha’awa shine yadda mata suka maida hankali a harkar neman ilimi, duba da yadda a da ba’a damu da neman ilimi ba, a yanzu abin ya sauya mata na kokarin kawo cigaba a alummarsu ta hanyar jajircewa, da marawa 'yaya da iyaye ke yi wajen neman ilimi.
Baraka ta ce daga cikin abubuwan da suka ja hankalinta har ta karanci aikin jarida, shine yadda take ganin aikin na sauya alkibilar alumma tare da kawo canji. Tana fatar a gaba ta bada nata irin gudunmawar wajen ganin ta kawo cigaba ga al'ummar ta.
Your browser doesn’t support HTML5