‘Yar wasan kwallon Tanis Serena Williams, ta bayyana cewar “Da sauran rina a kaba” bayan shan kashi da tayi a hannun yayarta Venues Williams, a wasan da suka gwabza a zagaye na uku a jihar Indiana.
Tsohuwar ‘yar wasan tanis din data kwashe tsawon lokaci tana hutu, biyo bayan haiwa da tayi, tun dai a farkon shekarar 2017 da tayi wasa da ‘yar uwar ta, basu sake haduwaba domin wani wasa ba.
Serena, ta ce lallai sai ta tashi tsaye don ganin ta koma matakin da take, na daya a duniyar wasan tanis, duk dai da cewar zai dauketa lokaci kamin jikinta ya koma dai-dai.
Ta kara da cewar “abin dadi ne mutun ya buga wasa bayan tsawon lokaci bai buga ba, da kuma kokarin tunawa da wasu dubarun wasa, don shirya ma gaba” kana kuma, wannan shine wasan da ta taba bugawa kuma ta sha kaye, amma taji dadin sa.