Yayin da masu kai ziyarar ibada ta mabiya tafarkin Mouride ke ta dunguma zuwa birni mai tsarki na Touba a kasar Senegal don ayyukan ibada na Magal, hukumomi na damuwa kan yiwuwar hakan ya yada cutar corona.
WASHINGTON, D.C. —
Hukumomi a kasar Senegal na fatan ayyukan ibada da za a yi na Magal, a birni mai tsarki na Touba, ba za su yada cutar corona ba.
Dubun dubatan masu ibada sun hallara don yin wannan ziyarar ibada ta Magal, inda ake mubaya’a ga wanda ya kirkiro akidar nan ta Mouride, wadda ta zama akidar addini mafi tasiri a Senegal.
Kodayake, saboda annobar ta corona, ba a tsammanin wannan karon wannan hidima ta addini za ta iya janyo jama’a da yawa, kamar yadda ta yi a baya, hukumomi a wannan kasa ta Yammacin Afirka na cigaba da nuna damuwa kan yiwuwar samun barkewar COVID-19 sanadiyyar wannan sha’ani na addini.