Senatocin Amurka Sun Sabunta Kira Ga Shugaba Trump A kan Sabbin Takunkumi A kan Rasha, Iran da Koriya Ta Arewa

Senatocin Amurka

Jiya Talata, senatocin Amurka suka sabunta kiraye kirayen ga shugaba Donald Trump, da ya sanya hannu nan take kan dokar da ta kunshi sabbin takunkumin da suka kakakabawa Rasha da Iran, da kuma Koriya ta Arewa,

Dukacin majalisun dokokin kasar guda biyu suka amince da wannan mataki da gagarumar rinjaye a makon jiya.

Fadar White House ta shugaban Amurka ta sha nanata kudurin shugaban na AMurka cewa zai sanya hannu kan kudurin domin ta zama doka, sai dai bata tsaida ranar da shugaban na Amurka zai yi haka ba, kuma fadar bata bada wata sanarwa na shirya bikin sanya hannu kan dokar wadda ya kan kunshi wakilan majalisun ba. Matakin da tuni ya janyo martani daga kasar Rasha.

A ganawa da manema labarai da fadar take yi a ko wace rana, mukaddashiyar sakataren yada Labarai Sarah Huckabee Sanders ta tabbatar d a cewa har yanzu shugaban na Amurka bai sanya hannu kan dokar ba.