Sean Connery Da Aka Fi Sani Da "James Bond" Ya Rasu

Marigayi Sean Connery.

Fitaccen jarumin nan dan asalin kasar Scotland Sean Connery, wanda ya samu daukaka da fina-finan “James Bond” cikin gomman shekaru da ya kwashe yana harkar fim, ya rasu. Shekararsa 90.

A yau Asabar Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito kafofin yada labarai na BBC da Sky News wadanda suka ba da labarin rasuwar Connery.

First Ministan kasar Scotland, Nicola Sturgeon, ta ce, “kasarmu na alhinin rashin daya daga cikin fitattun ‘ya’yanta.” Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Masu bibiyan fina-finan marigayi Connery za su fi tunawa da shi da fim din da ya fito a matsayin jarumin jami’in leken asirin Birtaniya da aka fi sani da 007, wanda marubucin kagaggun labarai Ian Fleming ya kirkira, wanda kuma da Connery yake fitowa a matsayinsa, inda ya fira fitowa a fim din “Dr. No” a shekarar 1962.

Marigayin ya yi ritaya da harkar fina-finai ne a shekarar 2003 bayan da suka samu sabani da darektan fim dins ana karshe “The League of Extraordinary Gentlemen.”