Harin ya kasance na bazata ne wanda aka kaiwa ‘yan majalisar jami’yar Republican, a lokacin suna atisayen wasan Baseball a gefen Washington.
Shugaba Trump wanda ya ziyarci Scalise a asibitin da yake jinya a Washington, jim kadan bayan harbin, ya ce ya na da kwarin gwuiwar zai samu sauki.
Dan majalisar ya kasance a cikin mawuyacin hali bayan wani aiki da aka masa, lamarin da ya sa likitocinsa suka fada a wata sanarwa cewa zai bukaci wani aikin a karo na biyu.
A matsayinsa na kasancewa mai tsawatarwa a bangaren masu rinjaye, scalise shi ne mutum na uku cikin jerin mutanen dake da karfin ikon fada a ji a majalisar wakilan Amurka.
James Hodgkinson, wato Dan bindigar da ya kai harin mai shekaru 66, ya fito ne daga birnin Belleville, na jihar Illinois, ya kuma rasa ransa bayan musayar wutar da suka yi da ‘yan sanda a lokacin da ya kai harin.