Sayfullo Saipov da ya nika mutane da mota a New York an sameshi da aikata laifuka 22

Sayfullo Saipov wanda ya hau kan mutane da mota a New York har ya kashe takwas da sunan kungiyar ISIS

Sayfullo Saipov shi ya tuka mota ya bi hanyar kekuna ya hau kan mutane takwas da ya kashe har lahira kana ya yi ikirarin niyar kashe fiye da haka a madadin kungiyar ISIS

Wasu masu taimakawa alkali yanke hukunci a matakin tarayya, sun amince da samun Sayfullo Saipov da aikata laifuka 22, sanadiyar mutuwar da wasu mutane takwas suka yi a lokacin da ya tuka wata babbar mota ya bankade su a wata hanya da aka tanada domin masu tuka kekune a Birnin New York.

Ma’aikatar shari’a ta ce an samu Saipov da laifi a jiya Talata a kotun ta tarayya da ke Manhattan.

An caje shi da aikata laifuka takwas na kisan kai, da laifin niyyar aikata kisa 12, da kuma niyya da tallafawa kungiyar IS hade da barnata motocin hawa da suka haifar da kisa.

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin motar, wanda shi ne mafi muni da aka kai Birnin na New York, tun bayan harin ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001.