Sakamakon ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa da fari da sauran ababen dake da alaka kai tsaye da sauyin yanayi suka jawo bala'o'in da hadura.
Farfasa Alhassan Mamman Muhammad na Jami'ar Abuja ya yi bayani akan sauyin yanayi. Yace sauyin yanayi kan sa ruwan tafki ya ragu ko kuma rafi ya kafe gaba daya.
Cikin wani rahoto da ta kira yadda dan Adam ya dandana kudarsa saboda sauyin yanayi Majalisar Dinkin Duniya (MDD) tace daga shekarar 2005 zuwa watan Augustan wannan shekara kimanin mutane dubu dari shida ne suka rasa rayukansu saboda canjin yanayi yayinda kuma mutane biliyan daya da miliyan daya ko sun ji rauni ko kuma sun rasa gidajensu a duk fadin duniya.
Farfasa Alhassan ya bayyana abubuwan da kan haddasa canjin yanayi. Fannin kimiya da fasaha da sinadari da ake kerawa domin jin dadin rayuwa su kan kara dumamar yanayi. Misali iskar da shuka ke fitarwa ita muke shaka yayinda su kuma suna shakar wadda muk fitarwa ta yadda muke nunfashi.
Aikace aikacen kamfanonin dake hako man fetur na taka rawa gaya wurin sauyawar yanayi.
Yanzu dai ana taron canjin yanayi a kasar Faransa inda shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kasance cikin masu halartar taron.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5