Sauya Shekar Gwamna Matawalle: PDP Ta Kira Taron Gaggawa

  • Murtala Sanyinna

PDP, APC

Jam’iyyar PDP ta ce gwamnan na ta bai shaida mata cewa yana kudurin barin jam’iyyar ba, haka kuma akwai shakku akan ko sauya shekar gwamnan ta dace da tanadin doka, la’akari da yadda ya sami darewa kan kujerar ta gwamnan jihar.

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ya kira wani taron gaggawa a ranar Litinin, bayan da aka ba da sanarwar cewa gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle zai kaddamar da komawarsa jam’iyyar APC a hukumance a gobe Talata.

Wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai na jihar ta Zamfara Ibrahim Dosara ya fitar, ta ce “gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da wasu manyan kusoshin jam’iyyar ta APC ne za su karbi gwamna Matawalle zuwa jam’iyyar ta APC.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Gwamnatin Zamfara)

To sai dai jam’iyyar PDP ta ce gwamnan na ta bai shaida mata cewa yana kudurin barin jam’iyyar ba.

Hakan kuma na haifar da shakku akan ko sauya shekar gwamnan ta dace da tanadin doka, la’akari da yadda ya sami darewa kan kujerar ta gwamnan jihar.

Karin bayani akan: APC, PDP, gwamnan, jihar Zamfara, Kotun Koli, Bello Matawalle, Abdullahi Umar Ganduje, Nigeria, da Najeriya.

Idan za’a iya tunawa dai Kotun Koli ce ta yanke hukuncin da ya karbe kujerar ta gwamna da dukkan mukaman takarar siyasa da aka ayyana jam’iyyar APC ta lashe a zaben shekarar 2019, ta kuma baiwa jam’iyyar PDP da ta zo ta biyu a yawan kuri’u a zabukan.

Hukuncin na kotu ya biyo ne bayan karar da wasu 'yan takara 8 na jam'iyyar ta APC suka shigar kan zargin rashin gudanar da sahihin zaben tsaida 'yan takara a jam'iyyar a jihar.

Wasu masana doka dai sun bayyana cewa jam’iyyar PDP ce kotu ta baiwa wannan mukamin ba Bello Matawalle ba, duk da yake wasu na da ra’ayi akasin wannan.

Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan (Twitter/ PDP)

To sai dai tuni gwamnan ya ture wannan cece-kucen a gefe, inda ya kammala dukan shirye-shiryensa na kulla sabon aure da jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

Wasu manazarta sun bayyana ra’ayin cewa gwamnan ya yanke shawarar komaea APC ne, domin a can ne ya fi yakinin samun damar zarcewa a wa’adin mulki na 2.

Saukar da kwamishinoni da gwamnan ya yi a ranar 31 ga watan Mayu na daga cikin shirye-shirye na karshe da suka bayyanar da matsayar gwamnan na sauya shekar.

A yanzu dai hankali ya karkata ne akan matakin da jam’iyyar ta PDP da ke da’awar ita ce aka baiwa mukamin na gwamna za ta dauka, da kuma makomar jam’iyyar ta APC da ta dade tana fuskantar rikicin da cece-kuce a jihar, wanda shi ne ma yayi sanadiyyar ta rasa kujerar ta gwamna da kuma dukkan sauran mukaman da aka yi takara a zaben na 2019.