Wani jami’in ofishin jakadancin Saudiyya da ke Najeriya da bai so a ambaci sunansa ba saboda ba shi da izinin yin mu’amala da kafafen yada labarai, ya ce masarautar ta dauki matakin ne don hana ci gaba da yaduwar cutar.
Saudiyya ta bayana mutum na farko da ya harbu da Omiron a matasyin wani fasinja da ya dawo daga Arewacin Afirka. Har ila yau, takunkumin na Saudiyya ya zo ne lokacin da Najeriya ta tabbatar da mutum na biyar da ya harbu da sabon nau'in.
Wata majiya mai tushe daga Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta kuma tabbatar da dakatar da fasinjojin da ke shigowa Masarautar daga Najeriya kamar yadda wasu majiyoyi suka rawaito.
Majiyar, wacce ta bayyana cewa NAHCON na ci gaba da sa ran samun sanarwa a hukumance daga hukumar Saudiyya game da sabuwar dokar hana zirga-zirgar, amma ta dage cewa matakin ba zai kawo cikas ga shirye-shiryen hukumar na aikin hajjin 2022 ba.
Haka kuma wani wakilin balaguro a Kano, Abdulazeez Sabitu, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce kamfanin jirgin na Saudiyya ya aika da sanarwar ga duk wasu ma’aikatan da ke Kano game da dokar hana zirga-zirgar.