Bayan an kai hari wurin jana'iza a Yamal jami'an Saudiya sun gina shigaye a harabar suna hana shiga ko fita daga wurin lamarin da ya jefa wadanda suka samu rauni cikin wani mawuyacin hali
WASHINGTON DC —
A halin yanzu Saudi Arabiya tace zata cire shingaye dake kan hanyar zuwa yankunan yan tawayen a Yemen don bada daman kwaso wadanda suka samu raunuka a wani farmaki da aka kai wurin wata jana’iza, idan har wani taimakon gaggawa bai samu shiga Yemen ba, a cewar wani mai pashin baki, saboda mutanenta da dama ne zasu fada cikin nan ba da dadewa ba.
Yace a kowace rana ta Allah al’amura na dada yin muni ne, inji Peter Salisbury wani jami’in nazari a kan Gabsa ta Tsakiya da Arewacin Amurka a wata cibiyar nzarai ta Chatham House dake Birtaniya.
Kungiyoyin bada agaji sun ce rabin al’umman Yemen suna fama da tamowa kuma kasha 80 cikin dari na mutanen kasar nada bukatar gaggawa na abinci da ma wasu bukatun.