Saudi Arabia Ta Karama Shugaba Donald Trump

Shugaba Donald Trump da sarki Salman

An dai dauki matsanantan matakan tsaro a filin jirgin saman da shugaba Donald Trump ya sauka inda aka warwatsa soja dauke da makamai.

A yau Assabar ne sarki Salman Bin Abdulaziz na Saudi Arabia ya baiwa shugaban Amurka Donald Trump lambar girma mafi fifiko ta Sa’udiyyar, a lokacinda su biyun suka gana a fadar shugaban na Sa’udiyya dake Riyadh, babban birnin kasar.

A yau din nan dai shugaba Trump ya isa kasar ta Saudiyya don soma ziyararshi ta farko zuwa kasashen ketare tun bayanda aka zabe shi.

Shi kansa sarkin Sa’udiyyar salman ne da kansa yaje har filin jirgin sama don tarbo Trump da matarsa Melania lokacinda suka isa.

A duk tarihin Amurka dai, ba’a taba samun shugaban Amurka da ya fara kai ziyararsa ta farko zuwa kasashen ketare da share fage da ita Saudi Arabia din ba.

Haka kuma abin yana da karin ban mamaki idan aka yi la’akari da kalamai da matakan da shi Trump din ya dauka akan Musulmi da yayi barazanar zai ma hana musu shiga Amurka din.

Sai dai kuma yayinda yake fara wannan balaguron farkon nashi zuwa kasashen ketare, a nan Amurka, farin jinin shugaba Donald Trump a wurin Amurka sai dada raguwa yake yi, har ma tagomashin nasa yayi faduwar da bai taba yi ba tun bayanda aka zabe shi, ko a tsakanin ‘yan jam’iyyarsa na Republican masu zabe.

Sakamakon binciken da kampanin dillacin labaran Reuters da cibiyar PSOS suka sako ya nuna cewa kashi 38% na Amurka ne kawai ke goyon bayan shugaban a yanzu, ayyinda kashi 56% ke cewa basa jin dadin kamun ludayinsa.

Saurian 6% kuma suka ce “basa da tabbas” na ainihin yadda suke ji gameda shugaban nasu.

An dai dauki ra’ayoyin mutane kamar 2,000 ne tsakanin rannaku 14 zuwa 18 ga watan nan na Mayu, lokacinda abubuwa kala-kala suka yi ta afruwa masu alaka da Trump.

A ranar Litinin aka fasa kwan cewa shugaba Trump ya baiwa jami;an gwamnatin Rasha wasu bayanan asiri na Amurka, kashegari ran talata aka fadi cewa tsohon shugaban FBI da aka kora James Comey ya bayyana cewa Trump yayi ta

matsa mishi ya jingine binciken da ake akan alakar kwamitin zaben sa da Rasha.

Kafin Laraba, ma’aikatar shara’a ta Amurka ta nada wani tsohon shugaban FBI Robert Mueller da ya jagoranci gudanarda binciken akan wannan alaka ta Trump da Rasha din.

Kafin Alhamis Trump ya fito yana kukan cewa ana binsa da “bakar yadiya”, kuma ba’a taba yiwa wanmi dan siyasa “wulakanci kamar yadda ake mishi ba.”