Daruruwan matasa a birnin Jos sun fito don gudanar da zanga-zangar fargad da gwamnati ta dauki kwararan matakan ba ‘yan sanda horo ta yadda zasu mutunta jama’a yayin gudanar da aikinsu.
Wadansu da suka gudanar da zanga-zangar sun ce suna bukatar gwamnati tayi wa wadanda jami’an SARS suka ci mutuncinsu adalci, ta kuma ba daukacin ‘yan sandan Najeriya horo da biya musu bukatunsu don su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
shahararrun-mutane-a-duniya-na-goyon-bayan-kanfen-din-yan-najeriya
yan-najeriya-sun-dage-sai-sun-ga-bayan-rundunar-sars
mun-dauki-matakin-farko-na-yi-wa-rundunar-yan-sanda-garambawul-a-najeriya
Zanga-zangar da tasa matasan toshe babbar hanyar da ta hada jahar Pilato da sauran sassan Najeriya, ta haddasa cunkoso a cikin garin Jos, lamarin da direbobi da fasinjoji suka rika kokawa.
A hirar shi da Muryar Amurka, kwamishinan yada labarai da sadarwa a jahar Pilato, Mr Dan Manjang yace gwamnati zata duba lamarin. Ya kuma yi kira ga matasa su kai zuciya nesa su kuma kiyaye doka da oda yayin gabatar da korafinsu.
Saurari rahoton Zainab Babaji cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5