Sarkin Waka Ya Ba Da Hakuri Kan Kalaman Da Ya Yi Akan ‘Yan Kannywood

Popular Hausa Singer Nazir Sarkin Waka (Instagram/Sarkin Waka)

"Wallahi, ban fadi wannan don na batawa wani sana’arsa ba, ko dan wani ya so ni ko dan wani ya kini." In Ji Sarkin waka

Fitaccen mawakin Hausa na zamani Nazir Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya fito ya ba da hakuri kan kalaman da ya yi wadanda suka ta da kura a masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya.

A ranar Alhamis mawakin ya fito shafinsa na Instagram ya furta wasu kalamai da ke nuni da cewa, sai an yi lalata da mata kafin a saka su a fim a masana’antar ta Kannywood.

Kalaman mawakin wanda ya yi a wani bidiyo mai tsawon minti 6:45, sun samo asali ne a martanin da ya yi kan rikicin da ya biyo bayan hira da BBC ta yi da jaruma Ladin Cima, wacce ta ce kudaden da ake biyan ta ba sa wuce dubu biyar, uku ko biyu, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Hirar ta Hajiya Ladin Cima ta sa furodusoshi irinsu Ali Nuhu, Falalu Dorayi suka yi tsokacin cewa sun taba biyan jarumar sama da kudaden da ta yi ikirarin ana biyan ta.

Martanin da Ali Nuhu da Falalu Dorayi suka yi, su suka harzuka Nazir Sarkin Waka ya wallafa bidiyonsa, inda ya goyi bayan Ladin Cima ya kuma dora da zargin cewa ana lalata da mata kafin a saka su a fim.

“A dauki dubu biyu a ba mutum a ce masa je ka za a turo, ba a turo, ko kuma mace a ce sai an yi wani abu da ita za a sa ta a fim, wannan magana haka take, ba karya ba ne, in kuma kun ji haushi an fada, ku kuka jawo.” Sarkin Waka ya ce.

Sai dai jim kadan bayan kalaman Nazir, wanda ya shahara da wakarsa ta “Mata Ku Dau Turame,” ‘yan masana’antar ta Kannywood sun yi masa ca akai suna kalubalantarsa.

Jarumai irinsu, Nafisa Abdullahi, Nuhu Abdullahi, Maryam Booth, Lawal Ahmad da dai sauran su, sun nuna fushinsu kan kalaman mawakin.

“Zantuttukan da Naziru Ahmad ya yi, manya-manyan zargi ne da ba’a daukan su da sanyi ko a ina ne, a ciki har da “cin mutunci ta hanyar lalata” wanda shi ne dalilin da ya sa na saka kaina h cikin abin da bai shafe ni ba….. Amma kuma idan aka yi la’akkari da abin da ya fada, ya shafe ni tunda mace ce ni.” In ji Nafisa Abdullahi.

Lamarin dai ya kai ga wasu rahoton sun nuna cewa, wasu har suna shirin maka mawakin a kotu kan zargin da ya musu na batanci.

Sai dai a ranar Lahadi, mawakin ya fito ya wallafa wani sabon bidiyo mai tsawon minti 11:40 inda ya ce an yi wa kalaman nasa mummunar fahimta.

“Ina so na dan ba mu hakuri ne a takaice, akan wannan abu, musamman mutanen gari, don Allah a yi hakuri, wallahi, wallahi, ban fadi wannan don na batawa wani sana’arsa ba, ko dan wani ya so ni ko dan wani ya kini.

“Ni dai Allah ya sani, har na gama maganar nan, ban kama sunan wani na zage shi ba, wadanda na kama sunayensu, misali na yi da abubuwan da suka fada.” Sarkin Waka ya ce.

Cikin jawabin nasa, mawakin ya kuma kara da yin alkawarin ba ladin Cima kyautar naira miliyan biyu don ta ja jari.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake jifan masana’antar ta Kannywood mai shirya fina-finan Hausa da kalamai makamanta wadannan ba.

Sai dai jarumai da shugabannin masana’antar wacce ginshikinta yake Birnin Kano a arewa maso yammacin Najeriya, sun sha musanta ire-iren wadannan zarge-zarge.