Kasancewar jihar Sokoto a matsayin daya daga cikin jihohin da suka fi sauran jihohi zaman lafiya a Najeriya, baisa hukumomi yin kasa a gwiwa ba wajan tunkara da fuskantar cece-kucen da ke barazana ga zaman lafiyar Najeriya a matsayin kasa daya al’umma daya, sakamakon martanin da matasan Arewa suka maidawa ‘yan kabilar Igbo, masu hankokron ballewa su kafa kasar Biafra.
Da yake jawabi gaban shugabannin kabilun dake zaune a jihar ciki harda ‘yan kabilar Igbo, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto Mohammed Abdulkadir, ya bayyana cewa kowa ya kwantar da hankalinsa domin Najeriya ta kowa da kowa ce a duk inda mutum yake zaune.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP Mohammed Ibrahim Abaras, ya bayyana cewa babban supetan ‘yan sanda ya zanta da manya manyan jami’an tsaro kuma ya bada umurnin gaggauta bada rahoton duk wata barazana ga wata kabila tare da bada lambobin waya domin shawo kan lamarin.
Shi da kansa, mai alfarma sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya amshi bakuncin kabilu mazauna jihar Sokoto, da dukkan hukumomin harkokin tsaron jihar domin yin buda bakin azumin Ramadan, kuma ya yi bayanin cewa idan aka yi la’akari da irin tashe tashen hankulan da ke faruwa a wasu sassan duniya, babu wanda zai yi farin ciki da irin tashin hankalin da ke kasancewa a kasar Syria, ko Iraqi ko Yemen da sauransu.
Domin karin bayani ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.
Your browser doesn’t support HTML5